Hukumar tattara kuɗin haraji ta kasa (FIRS) ta tara kimanin Naira Tiriliyan ₦4,952,243,711,728.37 a matsayin kuɗin harajin shekarar 2020.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban hukumar, Muhammad Nami, yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa.
Hakan na nuni da cewa hukumar ta samu kusan kashi 98% na kudin da gwamnatin kasar ta kiyasta wa hukumar ta FIRS ta samar a bangarenta a matsayin haraji na Naira tiriliyan 5.076.
