Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi FIRS ta tattara tiriliyan 4.178 cikin watanni 10

FIRS ta tattara tiriliyan 4.178 cikin watanni 10

44
0

Hukumar tattara kudaden haraji ta Nijeriya FIRS ta ce ta tattara kudin da suka kai darajar Naira tiriliyan 4.178 a karshen watan Oktoba, 2020, cikin tiriliyan 4.23 da ta yi hankoron tattarawa a cikin lokacin.

Jami’in kula da sashen haraji na hukumar Femi Oluwaniyi ne ya sanar da hakan a Abuja a lokacin ganawa da shugabannin kafafen watsa labarai.

Oluwaniyi yace yawan kudin da suka tattara ya kai kaso 99% na abin da suka yi hankoron tattarawa.

Yace sun kudurci tattara Naira tiriliyan 5.76 a cikin shekarar nan ta 2020.

Jami’in yace duk da dokar kulle ta “lockdown” dalilin cutar corona da aka sha fama da ita, hukumar ta iya tattara Naira bilyan 762 daga watan Afrilu zuwa Mayu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply