Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi FIRS ta tsawaita wa’adin biyan bashin haraji a Nijeriya

FIRS ta tsawaita wa’adin biyan bashin haraji a Nijeriya

119
0

Hukumar tattara kudaden shiga ta Nijeriya FIRS, ta kara tsawaita wa’adin rufe biyan bashin kudaden haraji a kasar.

A ciki wata sanarwa da Daraktan sadarwar hukumar Abdullahi Ahmad ya fitar a ranar Laraba, ya ce hukumar ta kara matsar da wa’adin yafiyar hukunta mutane da kamfanonin da ake bin bashin harajin tare da basu kafar biya, daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 31 ga wata Agustan 2020,

Ya yi bayanin cewa, shugaban hukumar Muhammad Nami, ya amince da kara wa’adin, a matsayin wani tallafin hukumar kan matakan farfado da tattalin arzikin kasar daga illar Covid-19.

Name, ya bukaci wadanda abun ya shafa, da su tuntubi masu karbar harajin, da kuma ofisoshin hukumar mafi kusa domin karin bayani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply