Home Siyasa Fulani ba ‘yan ta’adda bane inji Tinubu

Fulani ba ‘yan ta’adda bane inji Tinubu

137
0

Kisa A Kasar Yarbawa: TINUBU YACE FULANI BA YAN TAADDA BANE.

Jigo a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce shi bai son yaji ana zargin fulani da kidinafin a kasar yarbawa. Yace idan za a tsaya a fadi gaskiya kowa ya san inda kidinafin ya samo asali a Najeriya. Ya ce a don haka bai kamata a rinka yiwa dukkan fulani jam’i da cewa su ke aikata muggan laifuka a kudancin Najeriya ba.

Tibubu ya furta wadannan kalamai ne jim kadan bayan ya yiwa shugaban kungiyar Afeniferi taaziyyar kisan yarsa da aka yi makon nan mai kafewa. Kuma kisan wannan mata ya janyo zarge zarge masu muni da yan kudu kewa Fulani, inda wasu manyan kasar Yarbawa ke dora alhakin kisanta akan fulani duk da cewa babu wata hujja da ta nuna hakan.

Shin ya kuke kallon wannan furuci na Tinubu?

#ZuD

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply