Home Siyasa Dole fulani su kare kansu- Kungiyar Miyetti Allah

Dole fulani su kare kansu- Kungiyar Miyetti Allah

216
0

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta ce daga yanzu ya zama wajibi fulani da ke kiwon dabbobi a jihohin kudancin Najeriya su dauki matakin kare kansu da dukiyoyinsu.

Sakataren kungiyar Injiniya sale Alhassan ya shaidawa jaridar DCL Hausa cewa kungiyarsu na kira ga Fulani makiyaya da ke zaune a kudancin Najeriya da su kare kansu. Ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi ganin yadda kungiyoyin sa-kai, vigilantes, k eta yiwa Fulani makiyaya barazana a cikin ‘yan makonnin nan.

Kungiyar ta ce Fulani makiyaya a kudancin Najeriya dole ne su kare kansu don ba za su zauna ai ta kasha su babu kakkautawa. Injiniya Sale ya zargi kungiyar masu neman kafa kasar Biafra da kitsa duk wadannan matsaloli na tsaro a baya-baya nan, zargin da wannan jarida ba ita iya tabbatarwa ba.

A lokacin da jardidar tamu ta tambaye shi, ba ya ganin wannan mataki zai sa a zarge su da rura wutar rikici? Sai sakataren kungiyar … y ace “kare kai ba wai ya nuna nufin daukar makami ba. “ Za ka iya kare kan ka koda kuwa ka baka dauki makami ba.

 

Saurari muryar Injiniya Sale a nan kasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply