Home Labarai Fulani sun koka da ayyukan ƙungiyar sintirin Dakkarawa a Kebbi 

Fulani sun koka da ayyukan ƙungiyar sintirin Dakkarawa a Kebbi 

37
0

Makiyaya a kasar Zuru ta jihar Kebbi suna koka wa kan yadda suke zargin wata kungiyar Sintiri da Dakkarawa suka samar ke gudanar da ayyuka haramtattu ga makiyayan, inda makiyaya suke zargin muzgunawa da kuma wuce gona da iri ga ayyukan kungiyar Sintirin.

Kungiyar dai wadda Dakkarawa ne kadai ke iya zama wakilai a ciki na sosa zukatan al’umma musamman makiyaya inda ake ci gaba da samun takun saka da kuma kallon hadarin kaji ga bangarorin biyu.

Shima babban Daraktan kungiyar Miyetti Allah ta kasa Alhaji Bello Gotomo ya nuna rashin jin dadinsu ga wannan abu dake faruwa a kasar Zuru.

To amma a ta bakin Mani John mai magana da yawun kungiyar Sintirin ya ce suna kare kansu ne daga masu kokarin afka masu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply