Home Labarai Fyade: Kotu ta daure wani magidanci shekaru 10

Fyade: Kotu ta daure wani magidanci shekaru 10

137
0

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a garin Osogbo na jihar Osun a Talatar nan ta yanke wa Oyedokun Tunde mai shekara 34, hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari saboda samun sa da laifin yin lalata da wata yarinya ’yar shekara 13.

Alkalin kotun, Mary Awodele, ta ce kotun ta samu wanda ake tuhumar da aikata laifuka biyu da suka hada da cin zarafi da kuma fyade, hakan ya sa ta ba da umurnin a ci gaba da tsare shi a gidan gyara hali da ke Ilesa.

Tun da farko, dansandan da ya shigar da karar, ASP Abiodun Fagboyinbo, ya fada wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne tun a watan Afrilun shekarar 2018, a Yankin Omigbale na Osogbo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply