Home Kasashen Ketare Gambiya: Asirin Wani Sojan Yahaya Jammeh da ya Kashe Dan Jarida ya...

Gambiya: Asirin Wani Sojan Yahaya Jammeh da ya Kashe Dan Jarida ya tonu bayan shekaru 15

153
0

Daga: Saleem Ashiru Mahuta

 

Wani sojan kasar Gambiya Mai suna Laftanar Malick Jatta ya amsa laifin cewa yana daya daga cikin wadanda suka kashe ‘yan gudun hijira kusan 50 bisa umarnin Tsohon Shugaban kasar Yahya Jammeh, wanda a wancan lokacin ya zargi mutanen da cewar sunje don yi masa juyin mulki ne.

Sojan ya bayar da shaidar ne a gaban wani kwamiti da ke binciken irin barnar da aka yi a mulkin Yahya Jammeh na shekaru 22 kamar yadda BBC ta ruwaito.

 

Tun a baya, sojan ya bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka kashe wani dan jarida a 2004 mai suna Deyda Hydara wanda ya ce Mista Jammeh ne ya bayar da umarnin aiwatar da kisan, inda Jammen ya sha musanta hannu a kisan ‘yan ci-ranin.

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply