Home Labarai Ganduje na samar da lita milyan 900 ta ruwan sha duk rana...

Ganduje na samar da lita milyan 900 ta ruwan sha duk rana a Kano

134
0

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta na samar da litar ruwan sha milyan dari tara a kowace rana a fadin jihar, a yunkurin da ta ke na samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.

Shugaban hukumar samar da tsaftataccen ruwan sha na jihar Alhaji Garba Ahmed Kofar Wambai ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Kano.

Garba ya ce “gwamnatin jihar ta yi rawar gani, kan yadda ta samar da kayan aiki na zamani da kuma gyara abubuwan da suka lalace a matatun ruwa na jihar, hakan ya taimaka matuka wajen samar da tsaftataccen ruwan sha a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply