Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nada Idris Garba Unguwar Rimi a matsayin kwamishinan ma’aikatar ayyuka da tsara birane, tare canza wa wasu kwamishinoni ma’aikatu a ranar Larabar nan.
Hon. Mahmud Muhammad Santsi, daga ma’aikatar kasuwanci zuwa ma’aikatar tsara gidaje da zirga-zirga.
Barr. MA Lawan ya tashi daga ma’aikatar tsara gidaje da zirga-zirgar, zuwa ma’aikatar shari’a.
Barr. Ibrahim Lawan Mukhtar daga ma’aikatar shari’a zuwa ma’aikatar kasuwanci.
Malam Abba Anwar shi ne babban mai magana da yawun gwamnan jihar Kano ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta na Facebook.
