Home Labarai Ganduje ya kafa kwamitin tabbatar da rage kuɗin makaranta a Kano

Ganduje ya kafa kwamitin tabbatar da rage kuɗin makaranta a Kano

106
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi, wanda zai tabbatar da ragin kashi 25% na kuɗin makarantun kuɗi a jihar.

Kwamishinan Ilimi na jihar Muhammad Sa’id Ƙiru ya ƙaddamar da kwamitin ranar Alhamis, a ofishinsa da ke Kano.

Wata sanarwa da ta fito daga jami’in hudɗa da jama’a na ma’aikatar ilimin, Aliyu Yusuf ta ce Kwamishinan ya buƙaci wakilan kwamitin su tabbatar da makarantun sun yi biyayya ga umarnin gwamnati na rage kuɗin zangon karatu na uku.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply