Gwamnan jihar Kano ya sauke Kwamishinan Ayyuka na jihar Muazu Magaji daga mukaminsa. A cikin sanarwar cire Kwamishinan da Kwamishinan Labaran Jihar Kano ya fitar, gwamnati ta ce an cire Muazu Magaji saboda kalaman da ya rubuta a Facebook a kan mutuwar Abba Kyari.
Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Muazu Magaji ya yi rubutun da ke nuna cewa kamar yana murna da mutuwar marigayin.
