Home Labarai Ganduje ya musanta zargin dakatar da Murtala Sule Garo

Ganduje ya musanta zargin dakatar da Murtala Sule Garo

155
0

Gwamnatin jihar Kano ta ce wasikar da ke yawo a kafafen sadarwar zamani cewa an dakatar da Murtala Sule Garo, kwamishinan kananan hukumomi na jihar, ba ta tushe kuma babu kanshin gaskiya a ciki.

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan kafafen sadarwar zamani Salihu Tanko Yakasai ya fitar, ta ce kawai ana karda-kanzon-kurege ne a cikin wasikar.

Freedom Radio Kano ya rawaito cewa,Salihu Tanko Ykasai ya ce tuni ‘yansanda sun fara binciken inda wasikar ta samo asali domin kamawa tare da gurfanar da wadanda suka tsireta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply