Home Coronavirus Ganduje ya raba takunkumin fuska ga gidajen kallon ƙwallo

Ganduje ya raba takunkumin fuska ga gidajen kallon ƙwallo

104
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin a buɗe gidajen kallon ƙwallon jihar.

Ganduje ya bada wannan sanarwar ne a lokacin da shugabannin ƙungiyar masu gidajen kallon ƙwallo suka kai masa ziyara a ranar Juma’a.

Ƙungiyar ta roƙi gwamnan da ya sassauta masu dokar rufe gidajen da aka yi.

Nan take kuma Ganduje ya amince da hakan, tare da bada gudunmuwar takunkumin rufe fuska guda 40,000 don rabawa masu shiga kallon ƙwallon.

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar masu gidajen kallon ƙwallon Sharu Rabi’u Ahlan ya yabawa gwamnan kan ƙoƙarin sa na yaƙi da cutar coronavirus a jihar.

Wannan mataki dai na zuwa ne a daidai lokacin manyan gasar cin kofin Nahiyar Turai ke dawowa, kuma lokacin da alƙalumman masu kamuwa da cutar a Nijeriya ke ƙaruwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply