Home Labarai Ganduje ya sanar da rufe makarantun Kano

Ganduje ya sanar da rufe makarantun Kano

140
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ba da umurnin a rufe daukacin makarantun firamare da na sakandaren da ke jihar.

A cikin wata takarda daga kwamishinan ilmi na jihar Sanusi Kiru, ta shawarci iyaye da su fara shirin kwaso yaransu da ke makarantun kwana daga Larabar nan.

Kwamishinan bai ba da wata hujja ta matakin gwamnatin jihar na rufe makarantun ba, sai dai wasu na ganin hakan bai rasa nasaba da sha’anin tsaro.

Ko a ‘yan kwanakin nan, gwamnatocin Katsina, Jigawa da Zamfara sun ba da sanarwar rufe makarantun jihohin biyo bayan satar daruruwan dalibai da ‘yan bindiga suka yi a makarantar sakandaren kimiyya da ke Kankara jihar Katsina.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply