Home Labarai Ganduje zai gina wa Malaman makaranta gidaje 5,000

Ganduje zai gina wa Malaman makaranta gidaje 5,000

114
0

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta gina gidaje kimanin 5,000 ga malaman makarantar firamare da sakandire a fadin jihar.

Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron ganawa da iyayen kasa a jihar.

Ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne domin samar wa malaman makarantun da iyalansu matsugunni.

Gwamnan ya bayyana cewa za a gina gidaje 100 a kananan hukumomi 36 yayin da sauran kananan hukumomi 8 na cikin binni za a gina gidaje 150 a ko wace.

Ya kara da cewa ginin gidajen zai fara ne cikin sabuwar shekara mai kamawa karkashin hadakar gwamnatin jihar da bankin Mortgage.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply