Home Labarai Ganduje zai kashe milyan dubu 3 a yaki da maleriya

Ganduje zai kashe milyan dubu 3 a yaki da maleriya

114
0

Gwamnatin jihar Kano za ta yi hadaka da ƙungiyoyi masu zaman kansu inda za su kashe kimanin naira milyan dubu uku wajen rigakafin yakar zazzabin cizon sauro a jihar da ke saurin hallaka kananan yara da kuma mata masu dauke da juna biyu.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a ya yin wani taron bikin da aka kaddamar na yaki da zazzabin cizon sauro da ya gudana a fadar sarkin Bichi.

A karshe ya bayyana cewa gwamnatinsa na aiki tukuru wajen yaki da cututtukan da suka fi hallaka kananan yara da mata masu juna biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply