Home Labarai Ganduje zai yi wa dokar kafa masarautun Kano kwaskwarima

Ganduje zai yi wa dokar kafa masarautun Kano kwaskwarima

225
0

Gwamna Abdullahi Abdullahi Umar Ganduje na jihar kano ya gabatarwa majalisar dokokin jihar bukatar yi wa dokar masarautun jihar kwaskwasrima don ganin an kara sanya sunan Sarkin Dawaki Babba a matsayin jerin sunayen masu zaben sarkin a kano (king makers).

Shugaban majalisar na jihar Abdul’aziz Garba Gafasa ne ya karanta abin da da ke kunshe a cikin takardar da gwamnan ya aika masu a wani zama da majalisar ta yi a Larabar makon nan.

Sai dai kwamashinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa ganin yadda sarautar ta sarkin dawaki babba ke da karfin gaske ya sa gwamnan ya ga ya da ce a kara sanya ta daga cikin masu zaben sarkin na kano.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply