Home Labarai Gas ya kashe mutane takwas a Katsina

Gas ya kashe mutane takwas a Katsina

90
0

Mutane takwas ne rahotanni suka tabbatar da mutuwar su a Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Nijeriya a karshen mako.

A ranar Lahadi shaidu sun bada labarin cewa mutane takwas din sun hada da matan aure uku da yara kanana guda biyar.

Ana tunanin Gas din da ake girki da shi, Gas cylinder, shi ne ya fashe ya kuma tarwatsa har ya yi sanadiyar mutuwar mutanen.

Mai magana da yawun yan sanda a Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Trust.

Jama’a dai sun yi kokarin kai musu agaji lokacin da Gas din ya fashe wuta kuma ta ruru amma haka aka zurawa sarautar Allah ido saboda gidan yaqi budewa.

Daga baya rahotanni sun ce an tattaro gawawwakin jama’an an kuma yi musu jana’iza kamar yadda addinin Islama ya tanada.

 

 

Shin kana amfani da Gas? Me ya kamata mutane su yi don kaucewa fashewar Gas din?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply