Home Labarai Gbajabiamila zai biya diyyar ₦500m

Gbajabiamila zai biya diyyar ₦500m

112
0

Iyalan wani mai sayar da jarida Ifeanyichikwu Okereke sun bukaci Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da ya biya su doyyar ₦500m bayan ɗaya daga cikin jami’an dake bashi kariya ya bindige dan uwansu har lahira.

Sun bukaci hakan ne a cikin wata takarda da Lauyansu ya rubuta a ranar 23 ga watan Nuwambar 2020 bisa sahalewar Baban mamacin Okorie Okereke da sauran yan uwansa.

Iyalan mamacin sun kuma kirayi Kakakin majalisar da ya gaggauta gurfanar da jami’in gaban kuliya domin a bi musu kadi.

Tuni dai Kakakin majalisar Gbajabiamila ya ziyarci iyalan mamacin domin yi masu ta’aziyyar rashin da suka yi, ya kuma hannanta Abdullahi Hassan jami’in da ya yi harbin ga hukumar DSS domin gudanar da bincike.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply