Ministan harkokin waje na Nijeriya, Mr. Geoffrey Onyeama, ya harbu cutar coronavirus.
Geoffrey Onyeama shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafin sa na twitter ranar Lahadi.
“Onyeama ya ce an yi mani gwajinCOVID-19 har karo hudu a ranar Asabar, bayan da ya ji wasu alamun ciwon kai da mura.
