Home Coronavirus Gidaje 64,715, za su amfana da tallafin gwamnati a Neja – NEMA

Gidaje 64,715, za su amfana da tallafin gwamnati a Neja – NEMA

112
0

Kimanin gidaje 64,715 ne za su amfana da tallafin gwamnatin tarayya a jihar Niger.

Babban Daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Muhammadu A Muhammed ya bayyana haka a birnin Minna, lokacin da yake miƙa kayan tallafin ga gwamnatin jihar.

Muhammad wanda ya samu wakilcin muƙaddashin Daraktan sashen jin ƙai na hukumar Dr Bandele Onimode, ya ce ya zo jihar ne don bada tallafin kayan waɗanda aka kawo daga rumbun ajiyar abinci na ƙasa bisa umarnin shugaba Buhari, domin raba wa ga masu ƙaramin ƙarfi.

Kayan abincin sun ƙunshi tan 1,490.36 na masara, tan 1,557.6 na Dawa da kuma tan 1,870.8 na gero.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply