Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Gidajen Biredi sun shiga yajin aiki

Gidajen Biredi sun shiga yajin aiki

153
0
biredi bread

Gidajen biredi a jihar Plateau sun fara yajin aikin kwana uku saboda tsadar filawa da sauran kayan hadin biredi a jihar.

DCL Hausa ta samu rahoton cewa da yawan masana’antun biredin sun rufe gidajensu domin shiga yajin aikin, wanda suka ce tsadar filawa ce ta janyo basa samun riba ko sunyi biredin.

Sai dai shugaban masu sarrafa fulawa a jihar Salis Abdallah ya ce mambobin kungiyar tasu sun rufe gidajen ne dan shara da kuma tsaftace muhallin sana’ar tasu. To amma wani d’an kungiyar ya shaida cewa sun rufe gidajen biredin ne dan shirin da suke na kara wa biredin kudi.

Da yake jawabi, wani mai sana’ar sayarda shayi a jihar ta Filato ya bayyana cewar dole ce tasa su rufe wurin sana’ar tasu sakamakon ba wanda zai sayi shayi in babu biredi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply