Home Addini Gidan Mari : Yan Sanda Sun Dira A Ilorin, Sun Kubutar Da...

Gidan Mari : Yan Sanda Sun Dira A Ilorin, Sun Kubutar Da Mutane 108 Daga Sarka

82
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”2t7o0qo8rv” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”p13tzygh0u” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”thsal0q73f” animation_delay=”0″]

Yan sanda a jihar Kwara sun bankado wata cibiya ta gyara kangararru mai suna Sumuratu Mumeen Arabic Centre da ke yankin Gaa-Odota a cikin garin Ilorin. Rundunar yan sandan jihar ta ce mutane 108 ta kubutar daga abin da ta kira keta musu haddi da ake musu a cibiyar.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya-NAN- ya ruwaito kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr Kayode Egbetokun yana sanar da wannan kame  a ranar alhamis.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce sun samu bayanai na sirri da ke nuna cewa cibiyar gyara halin ta kunshi dalibai maza guda 103 da mata guda 5 wadanda ake gallaza musu. Ya ce cibiyar ta kasance tamkar haramtaccen gidan kaso da ake ajiye mutane don a cutar da su domin wasu cikin daliban suna dauke da cututtuka amma kuma masu cibiyar sun gaza yi musu magani.

 

Sai dai ‘yan sandan sun ce bincikensu na farko farko ya nuna cewa iyayen daliban ne suka kai su cibiyar gyara halin. Sun kuma ce za su ci gaba da bincike amma kafin su kammala, daliban za su ci gaba da kasancewa a hannunsu don ba su kulawar likita.

 

Abdulazeez Korede yana cikin daliban, ya ce iyayensa ne suka kawo sa domin a gyara masa tarbiyya yadda zai daina shaye shaye amma a karshe sai aka ‘buge da gallaza masa. Ya yi zargin an rinka daure shi da sarka ana lakada masa duka na fitar hankali.

Hotan irin sarkar da ake daure mutane da ita a irin wadannan gidaje na gyara hali

Ita kuma Olaide Arikewuyo a matsayinta na daliba mace ta ce shekaru biyar ta kwashe a cibiyar kuma ta yi zargin wani wanda ke zaman baban mai cibiyar ya rinka yin jima’i da ita ba tare da amincewarta ba.

Ta kuma yi zargin bacin shi wannan mutum akwai wasu maza guda hudu da su ma suke kwanciya da ita. A sakamakon haka ta ce ta samu juna biyu kuma sau uku ana zubar mata da ciki.

 

Tun daga karshen watan Satumba dai ‘yan sanda su ke ta kai samame  a irin wadannan makarantu na gyara hali. A garin Kaduna sun kama makarantu guda 2, a garin Daura ma sun kama makaranta guda 1, a cikin garin Katsina guda 1, a jihar Adamawa ma an kai samame akan wata cibiya irin wannan. Sai kuma ga shi yanzu an dira a jihar Kwara.

 

Masu sharhi na cewa babu tabbas akan ko ‘yan sanda za su dakata haka domin a ranar 19 ga watan Oktoba Shugaba Buhari na Nijeriya ya bayar da umarni ga ‘yan sanda da su ci gaba da binciko irin wadannan makarantu suna fallasawa.

 

Sai dai a gefe kuda wasu da jaridar DCL Hausa ta tattauna da su na cewa sai anyi hattara sosai domin idan aka ci gaba da sako mutanen da kangararru ne ba tare da gwamnati ta yi wani tanadi ba to tamkar ta bude kofar ci gaba da aikata laifuka ne a kasar.

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply