Home Labarai Gidan Sunday Igboho ya kama da wuta

Gidan Sunday Igboho ya kama da wuta

33
0

Ɗaya daga cikin gidajen Sunday Igboho da ke unguwar Soka a Ibadan ya kama da wuta da sanyin safiyar Talatar nan.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya rawaito cewa wutar wadda ba a san miye silarta ba, ta lalata kaya na miliyoyin Nairori.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an kashe gobara na jihar Oyo sun zo wurin sa’o’i kaɗan bayan tashin wutar.

Da yake magana da NAN Daraktan ayyuka na hukumar Isma’il Adeleke, ya ce ɗakin hutu da wani koridon gidan ne wutar ta shafa saboda saurin isowar jami’an kashe gobarar, kuma babu wanda ya rasa ransa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply