Home Labarai Gobara Ta Cinye Rumfuna 252 A Kasuwar Abuja

Gobara Ta Cinye Rumfuna 252 A Kasuwar Abuja

87
0

Akalla shaguna 252 na wucin gadi ne suka kone a gobarar da ta tashi a Kasuwar Galadima da ke Gwarimpa, Abuja.

Da misalin karfe 1:30 na rana ne gobarar ta tashi lokacin Musulmai sun tafi Sallar Juma’a takwarorinsu Kiristoci kuma suna hutun Kirsimeti.

Wata daga cikin ’yan kasuwar Falmata Bukar ta ce gobarar ta tashi ne bayan an dawo da wutar lanatarki, kan ka ce kwabo wata waya ta fara tartsatsin wuta shaguna suka fara ci.

Fatima ta ce gaba daya jarinta a shagonta na sayar da abinci da kayan tireda a kasuwar ya kone kurmus a gobara.

Wani tela ya shaidawa majiyar DCL Hausa cewa kekunan dinkinsa da kayan mutanen da suka kawo masu dinkin duk sun kone a gobarar.

Shugaban kasuwar, Sulaiman Musa, ya ce gobarar ta lakume kaya na miliyoyin Naira.

Ya ce tawaga uku na masu kashe gobara ne suka bayar da dauki da suka hada da na Birnin Tarayya, Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) da Rundunar Sojin Sama, duk sun isa wurin domin hana gobarar kama sauran gine-ginen da ke makwabtaka da kasuwar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply