Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Sabon Gari cikin kwaryar Zariya a jihar Kaduna da safiyar ranar Asabar.
Wani shaida da ya ganewa idomsa, Alhaji Abbas Abdullahi, ya fadawa jaridar Blueprint cewa gobarar ta shafi shaguna 8 inda ta yi sanadiyyar lalata kadara ta miliyoyin Nairori.
Alhaji Abdullahi ya ce duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba sakamakon saurin kai dauki da jami’an kashe gobara na Zariya suka yi.
Ya kuma ce sun yi nasarar kashe gobarar cikin sa’a daya.
