Home Sabon Labari Gobara ta lalata wasu gine-gine a barikin sojoji na Depot da ke...

Gobara ta lalata wasu gine-gine a barikin sojoji na Depot da ke Zaria

54
0

Wata gobara ta lalata ginin da sojoji masu mukamin kofur (corporal) da  ke zama a barikin sojoji na Depot da ke Zaria jihar Kaduna arewacin Nijeriya. Mai magana da yawun Depot Nigerian Army Zaria, Arigu Audu ya shaida wa DailyTrust cewa gobarar ta samo asali ne daga wutar lantarki. Ya ce babu rasa rayuka da aka samu.

Lamarin ya faru ne dai a ranar Asabar da misalign karfe tara na dare (9pm) kuma acewar Mr Audu jami’an soji da ke lura da kashe gobara da hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna sun yi kokarin kashe wutar duk da ta riga ta lalata benen karshe na ginin da gobarar ta faru. Sai dai ya ce tuni aka kaddamar da bincike domin gano karin bayanai dangane da wannan lamari.

Barikin Depot Nigerian Army dai bacin samar da masauki ga kananan sojoji a nan ne kuma DCL Hausa ta fahimci cewa kuratan sojoji ke samun horan sanin makamar aikin soja na watanni biyar zuwa shida.

Labarai masu alaka: Depot Zaria: Sojoji sun gargadi masu son shiga aikin soja

Gobara ta tashi a kasuwar Sabon Garin Zariya

Gobara Ta Cinye Rumfuna 252 A Kasuwar Abuja

Gobara ta tashi a dakin ajiyar gawa ‘mortuary’ a Zamfara

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply