Gobara ta tashi a wani sashe na ginin cibiyar kasuwanci ta duniya da ke Abuja.
Sai dai babban jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta kasa Dsp Ugo Huan ya bayyana cewa tuni jami’an hukumar su ta kashe gobara suka kashe wanna wuta.
Har ya zuwa yanzu ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba .
