Home Labarai Gobara ta tashi a dakin ajiyar gawa ‘mortuary’ a Zamfara

Gobara ta tashi a dakin ajiyar gawa ‘mortuary’ a Zamfara

81
0

Gobarar ta tashi a dakin adana gawarwaki  “mortuary” na asibitin kwararru da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Babban likitan asibitin Dr Bello Muhammad Kotorboshi ya fada wa jaridar Daily Trust cewa ba a san musabbabin tashin gobarar ba, sannan an kafa kwamiti don bincikar musabbabin hakan.

Ya ce babu komai a dakin adana gawarwakin a lokacin da gobarar ta tashi, amma dai ta lalata kayan aikin da ke dakin.

Dr Bello ya ce tuni sun sanar wa ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa da kuma gwamnatin jihar game da tashin gobarar, ya ce kwamitin da aka kafa don bincikar lamari ya fara aiki.

Irin wannan tashin gobara ya taba faruwa a jihar Anambra a watan Disambar 2018, inda rahotanni suka ce gawawwakin mutane 50 wuta ta kurmushe su aka gaza gane su.

Sai dai wannan na baya bayan nan a jihar Zamfara, anyi sa’a wutar ba ta kona koda gawa daya ba.

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply