Home Labarai “Green House” ta karrama wakilin DW a Katsina

“Green House” ta karrama wakilin DW a Katsina

236
0

Kamfanin “Green House” da ke birnin Katsina ya karrama Yusuf Ibrahim Jargaba wakilin gidan rediyon DW Hausa da ke aike wa da rahotanni daga jihohin Katsina da Zamfara.
Kamfanin ya ce ya karrama Yusuf Jargaba ne duba da yadda ya ke aike wa da rahotannin da suka taba rayuwar al’umma kai tsaye.

Daruruwan mutane ne suka halarci bikin bayar da lambar yabon da ya gudana a dakin taro na Katsina Motel domin taya murna da karfafa guiwar ci gaba da gudanar da irin aikin da ya sa aka karrama shi.

Yusuf Ibrahim Jargaba a nasa jawabi, ya ce ya sadaukar da wannan lambar yabo ga gidan rediyon DW Hausa da sauran ma’aikatan wurin.

Kafar yada labaran DW Hausa mallakar gwamnatin kasar Jamus ce da ke yada shirye-shirye ta a rediyo da intanet daga birnin Bonn na yammacin Jamus.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply