Home Kasashen Ketare Guardiola zai ci gaba da zama Man City har 2023

Guardiola zai ci gaba da zama Man City har 2023

102
0

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya amince da sake kulla sabuwar yarjejeniyar kwantaragin shekara biyu.

Sabon kwantiragin dai zai kai Guardiola har zuwa karshen kakar wasanni ta shekarar 2023.

Man City ta dauko Guardiola daga kungiyar Bayern Munich a shekarar 2016, inda ya zuwa yanzu ya shafe kakar wasanni biyar a kungiyar kuma ya taimaka mata ta samu nasarar lashe kofin Firimiya har guda biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply