Home Sabon Labari Gudun Hijra: Nijeriya ta amshi mutane 158 cikinsu akwai mata masu juna-biyu...

Gudun Hijra: Nijeriya ta amshi mutane 158 cikinsu akwai mata masu juna-biyu 8 daga kasar Libya

70
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”ojvqlrpq8″ data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”hfwbx3b3c4″ data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”w0w1nnf21c” animation_delay=”0″]

 

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya ta amshi ‘yan Nijeriya daga kasar Libya su 158. Shugaban ofishin hukumar ta NEMA mai kula da kan iyakoki a birnin Legas Alhaji Idris Muhammad ya fada wa ‘yanjarida cewa sun amshi wadanda suka dawo din a madadin gwamnatin Nijeriya.

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN  ya ba da rahoton cewa wadannan rukunin da suka dawo daga kasar Libya sun iso Nijeriya ‘yan awanni bayan mutane 187 sun dawo daga kasar Afrika Ta Kudu.

 

Alhaji Muhammad ya ce, an mai do wadanda suka dawo daga kasar Libya ne ta jirgin Al Buraq da ya sauka a sashen saukar jiragen dakon kaya na filin jirgin Murtala Muhammad da ke Legas da misalin karfe 12:55 na dare.

 

Ya ce hukumar kula da ‘yan gudun hijra ta kasa da kasa da kungiyar tarayyar Turai ne suka dauki nauyi mai do ‘yan Nijeriyar gida.

 

Kididdiga ta nuna cewa akwai mata masu juna biyu 8 da yara mata 3 da yara maza 3 sai jarirai mata 5. Kazalika, akwai maza manya 84 da yara maza 5 da jarirai maza 5 tare da wasu marasa lafiya guda 7.

 

Nijeriya dai na ci gaba da amsar ‘ya’yanta daga kasashen Libya, Afrika Ta Kudu da ma wasu kasashen Turai wadanda mafi yawansu sun je ci-rani ne. Ko ya makomar irin wadannan jama’an za ta kasance a Nijeriya yanzu da suka dawo gida?

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply