Sheik Ahmad Gumi ya yi kira da a nisanta addini daga siyasar jam’iyya, yana mai cewa bai kamata a rika amfani da bambancin addini wajen neman kuri’u ko rura rikicin siyasa a Nijeriya ba.
Gumi, wanda malamin addini ne da ke zaune a Kaduna, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tantance, yayin da yake mayar da martani kan kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir, shugaban JIBWIS na kasa.
A wani taron bikin auren-gata da aka gudanar a Kano ranar Asabar, Jingir ya kare tikitin shugaban kasa na jam’iyyar APC na Musulmi da Musulmi, inda ya bukaci al’ummar Musulmi su kada kuri’a ga shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda ya zabi abokin takararsa wanda suke da addini daya.
Kalaman Jingir sun jawo suka daga wasu shugabannin Kirista, kungiyoyin farar hula da masu fafutuka, wadanda suka bayyana cewa irin wannan matsaya na iya kara rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma.
Sai dai Gumi ya ce ya kamata a fahimci matsayar Jingir, yana mai cewa malamin yana furuci ne a wani yanayi da yake ganin ana nuna tsattsauran ra’ayi ga Musulunci. Duk da haka, ya jaddada cewa bai kamata a mayar da addini makamin siyasa ba.
Gumi ya kuma ce amfani da addini wajen neman kuri’u ba matsalar bangare daya ce kawai ba, yana mai cewa ‘yan adawa ma na iya amfani da batun addini wajen samun goyon bayan masu kada kuri’a.
Ya ce, “A cikin al’umma mai addinai daban-daban, bai kamata a jawo addini cikin kazamar siyasa ba,” tare da kira ga ‘yan siyasa da shugabannin addinai da su mutunta bambancin addinai da ke Nijeriya.
A gefe guda, reshen jihar Plateau na Jama’atu Nasril Islam (JNI) ya nesanta kansa daga kalaman da aka danganta wa Jingir kan batun tikitin Musulmi da Musulmi.
Sakataren yada labaran JNI na Plateau, Gambo Hamza, ya bayyana rahoton da ya ce kungiyar ta goyi bayan matsayar Jingir a matsayin karya da yaudara. Inda ya ce matsayar Jingir ra’ayinsa ne na kansa, ba matsayar kungiyar JNI ta Plateau ba.
