Yawan mutanen da suka mutu ta dalilin shan gurbatacciyar giya a kasar Indiya ya kai 105 a Litinin din nan.
Manoma da ma’aikata a jihar Punjab sun fara rashin lafiya biyo bayan shan wata giya da suka yi, da a ranar Larabar makon jiya mutum na farko ya fara mutuwa.
Ya zuwa ranar Juma’a yawan mutanen ya kai 21, bayan da wasu iyalai suka kai rahoton yawan mace-macen ga hukumomi.
Kwanaki 5 baya, sama da mutane 80 suka mutu a gundumomi uku na jihar ta Punjab.
