Zaharaddeen Umar
A cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye mai ba gwamnan jihar Kaduna shawara akan sadarwa ya fitar a ranar litinin din nan ya ce gwamnatin jihar Kaduna za ta fara biyan sabon albashi na Naira 30,000 daga ranar 1 watan Satumba.
Sanarwar ta ce wannan mataki ya biyo bayan matsayar da majalisar zartarwar jihar ta cimma a taron da aka gudanar a yau litinin.
Gwamnatin ta ce aiwatar da sabon albashin zai lakume kusan karin kudi Naira Bilyan Daya a kowane wata. Ta ce karin zai mayar da kudin da za su ke kashewa kan albashi a wata-wata zuwa Bilyan 3.759 daga Bilyan 2.827 da suke kashewa a baya.
Gwamnatin Elrufai ta ce aiwatar da karin albashin na nufin kudin gwamnati za su rika sulalewa zuwa wurin biyan albashi, duk da cewa jama’a na da bukatar a yi musu ayyukan raya kasa. A saboda haka gwamnatin ta ce za ta kara hanyoyin samun kudin shiga (haraji) don aiwatar da tsarin.
Tun a farkon wannan shekarar gwamnatin Nijeriya ta amince da sabon albashi wanda ya tanadi Naira 30,000 matsayin karancin albashin da za a ba kowane maaikaci a kasar, amma kuma ita kanta gwamnatin tarayya har yanzu ta gaza aiwatar da tsarin. Sai kuma ga shi yanzu gwamna Elrufai ya ce shi zai fara biyan maaikata wannan albashi
