Home Sabon Labari Gwamnatin Katsina ta dagargaza gidan wani gawurtaccen dan ta’adda a Kafur

Gwamnatin Katsina ta dagargaza gidan wani gawurtaccen dan ta’adda a Kafur

82
1

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin rushe gidan wani wanda ake zargi da zama gawurtaccen dan ta’adda a kauyen Yar Talata da ke cikin Karamar Hukumar Kafur ta jihar. Ibrahim Masaja wanda yan sanda suka ce ya gawurta wurin aikata muggan laifuka a jihar katsina, ana zargin ya hada baki da wasu ‘yan ta’adda wurin yin garkuwa da wani mutum mai suna Paul Lawal.

Kidinafas din acewar ‘yan sanda sun sace Paul a ranar 04.01.2020 inda kuma suka kawo shi gidan Ibrahim Musa a kauyen ‘Yar Talata suna bukatar a ba su Naira Milyan 15 a matsayin kudin fansa.

Gidan wanda ake zargi da ta’addancin ke nan a lokacin da jami’an tsaro suka cinna gidan wuta

 

Sai dai mai magana da yawun ‘yan sanda SP Gambo Isa ya ce ‘yan sanda sun yi barin wuta bayan da suka gano abin da ake aikatawa a gidan Ibrahim Masaja din. Ya ce jami’an yan sanda na musamman da ke yaki da kidinafin, SARS, sun kama wani mutum guda daya da suke zargi, sannan rayuka biyu sun salwanta a lokacin ‘bata-kashin’. A gefe guda kuma shi mai gidan da ake aikata kidinafin din ya arce. Amma ‘yan sanda na ci gaba da nemansa.

Jami’an tsaro ke nan ke sintiri bayan da suka ruguza gidan Ibrahim Musa a kauyen Yar Talata da ke Karamar Hukumar Kafur.

Abdullahi Aliyu Yar’adua mai magana da yawun Sakataren Gwamnatin jihar Katsina ya ce bayan da tawagar jami’an tsaro da ta hada da; sojoji da ‘yan sanda suka ruguza gidan dan ta’addar a bisa umarnin Gwamna Masari, jama’a sun fito kan hanya a kauyen Malamawa suna murna, suna furta cewa “nasara ta zo” suna masu godewa Gwamna Aminu Bello Masari a kan kwararan matakan da yake dauka don murkushe ‘yan ta’adda a baya bayan nan.

 

Kalli wasu hotunan gidan da aka rusa

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply