Home Labarai Gwamna ya bada umurnin gaggauta buɗe kasuwar Shasha

Gwamna ya bada umurnin gaggauta buɗe kasuwar Shasha

30
0

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya bada umurnin hanzarta buɗe kasuwar Shasha nan take.

Gwamna Makinde dai, shi ya bada umurnin rufe kasuwar biyo bayan rikicin ƙabilanci da ya yi silar rasa rayukan da ɓarnata dukiyoyi.

Wannan umurni na sake buɗe kasuwar ya zo ne lokacin da Gwamnan yake ganawa da sarakunan yankin da suka haɗa da Baale na Shasha da Sarkin Hausawan Shasha a ɗakin taro na Sakatariyar jihar da ke Ibadan a ranar Talatar nan.

Gwamnan ya ce duba da halin tattalin arziƙi da ake ciki da kuma sanin da aka yi wa jihar ya sanya ya bada umurnin buɗe kasuwar domin ƴan kasuwa su ci gaba da harkokinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply