Home Labarai Gwamnan Bayelsa zai ɗaukaka ƙara kan soke zaɓensa

Gwamnan Bayelsa zai ɗaukaka ƙara kan soke zaɓensa

132
0

Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, ya ce zai ɗauka ƙara kan hukuncin da kotun sauraron ƙrarrakin zaɓe ta Abuja ta yanke a ranar Litinin, wanda ta soke zaɓensa.

Gwamnan wanda ya bayyana haka jim kaɗan bayan yanke hukuncin kotun, ya ce ya buƙaci lauyoyinsa su tattara duk takardun da ake buƙata na ɗaukaka ƙarar.

Wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Daniel Alabrah ya fitar, ya ambato Diri na cewa, yana da ƙwarin guiwar yin nasara a shari’ar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply