Home Sabon Labari Gwamnan Gombe ya bukaci shugabannin kananan hukumomi su guji cin hanci

Gwamnan Gombe ya bukaci shugabannin kananan hukumomi su guji cin hanci

73
0

Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya gargadi sabbin shugabannin kananan hukumomin da aka rantsar a jihar da su guji cin hanci da rashawa.

Gwamna Inuwa Yahaya, ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin, yayin rantsar da shugabannin kananan hukumomi su 11.

“Ina umartarku da ku kasance masu adalci, gaskiya da rikon amana, ku nuna daidaito da adalci ga dukkan‘ yan ƙasa ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko al’ada ba” inji gwamnan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply