Home Sabon Labari Gwamnan Katsina ya bukaci sojoji su kama ko harbi duk mai tuka...

Gwamnan Katsina ya bukaci sojoji su kama ko harbi duk mai tuka babur a daji da daddare

105
0

Gwamnan jihar Katsina Aminu  Bello Masari ya bukaci Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Airforce da ta harbe duk wani wanda suka gan shi yana tuka babur da daddare a cikin dazukan da ke jiharsa.

Hassan Muhamamd Tukur wani dan jarida  da ke aiki a bangaren yada labarai na gidan gwamnatin jihar Katsina ya sanar da haka. Ya ce gwamnan ya yi wannan furuci ne a ziyarar da ya kai wa Air Vice Marshall Sadiq Abubakar Shugaban Rundunar Sojin Sama a ofis dinsa da ke Abuja a ranar Litinin din nan.

Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa a lokacin da ya ke sanar da jama’a cewa gwamnati za ta rufe kofar yin sulhu da ‘yan bindiga.

Gwamna Masari ya shaida wa shugaban sojan sama na Nijeriya cewa a makon da ya gabata dokar takaita hawa babura ta fara aiki. Ya ce gwamnati ta bukaci kada wani ya hau babur a tsakanin karfe 7 na yamma zuwa 6 na Safiya. Ya ce a don haka sojoji su dauki duk wanda suka gani yana tuka babur da daddare a matsayin dan bindiga wanda gwamnati ke nema ruwa ijallo. Ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne a ci gaba da kokarinta na kawar da matsalar garkuwa da mutane da kashe-kashen jama’a a yankunan karkara.

A farko farkon watannan ne dai gwamnatin jihar Katsina ta sanar da rufe kofa ga duk ‘yan bindigar da suka ki rungumar shirinta na sasanci da yin afuwa wanda ta bude wurin shekaru uku ke nan. Tun daga lokacin gwamnati ke daukar matakai dabam-dabam  na murkushe ‘yan bindigar da karfin tuwo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply