Home Labarai Gwamnan Lagos zai dakatar da fanshon tsaffin gwamnonin jihar

Gwamnan Lagos zai dakatar da fanshon tsaffin gwamnonin jihar

77
0

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya yi kiran da a yi gyaran fuska da dokar fanshon jihar ta 2007, wadda ta bada damar biyan fansho da sauran wasu hakƙoƙi ga tsaffin gwamnonin jihar.

Gwamnan ya yi kiran ne a lokacin da yake gabatar da ƙudirin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2021 a gaban majalisar dokokin jihar, ranar Talata a Ikeja.

Ya ce nan ba da jimawa ba zai aiko da ƙudirin doka ga majalisar kan wannan batu, wanda idan ya samu amincewar Majalisar, tsaffin gwamnonin jihar irinsu Bola Tinubu, Babatunde Fashola, Akinwumi Ambode za su daina karɓar kuɗin fansho.

A cewar Sanwo-Olu, matakin zai taimaka wajen rage kuɗin da gwamnati ke kashewa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply