Home Labarai Gwamnan Nasarawa zai yi jinyar kwanaki 17 a ketare

Gwamnan Nasarawa zai yi jinyar kwanaki 17 a ketare

65
0

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sanar da majalisar dokokin jihar cewa zai yi tafiya zuwa Amurka don duba lafiyarsa daga 13 ga Disamba zuwa 29 ga Disamba.

Shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Ibrahim Balarabe-Abdullah ne ya bayyana hakan a zaman majalissar.

Wasikar na kunshe da, “Ina so in sanar da mai girma shugaban majalisa cewa, zan yi tafiya zuwa Amurka don duba lafiya daga Lahadi, 13 zuwa Asabar 29th Disamba 2020.

“A sakamakon haka, mataimakin gwamna zai kula da harkokin jihar har sai na dawo,” in ji gwamnan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply