Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya warke daga cutar corona bayan ya kwashe sama da mako guda a inda ya ke a killace.
Akeredolu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke Akure.
Gwamnan ya kara da cewa likitoci sun tabbatar masa da cewa ya warke sarai bayan da sakamakon gwajin da aka masa har karo biyu ya nuna ba ya dauke da cutar.
