Home Sabon Labari Gwamnan Ribas ya dakatar da hukumar alhazai bayan ya ce ribas  jihar...

Gwamnan Ribas ya dakatar da hukumar alhazai bayan ya ce ribas  jihar Kiristoci ce

70
0

A labarin da jaridar intanet ta Sahara Reporters ta wallafa ta ruwaito Alhaji Abubakar Orlu, Mataimakin Shugaban Jama’atu Nasril Islam, (JNI), yana bayar da dalilin sauke shugabancin hukumar alhazan jihar Ribas da Gwamna Wike ya yi.

Labari mai alaka da wannan: Taskar Guibi: Labarai da Sharhi A Takaice 26.08.2019

Sahara Reporters ta ce a wata sanarwa da Alhaji Abubakar Orlu ya fitar a ranar Asabar ya ce Gwamna Wike ya dakatar da hukumar ne bayan da ya samu labarin damfara da danniya da ke gudana a bangaren aikin hajji a jiharsa ta Ribas. Mataimakin shugaban JNI din ya yi zargin jami’an hukumar alhazai ta jihar Ribas sun rinka sanya sunayen wasu Musulmi da ba ‘yan jihar Ribas ba a cikin alhazan jihar, abin da ya ke nuna cewa akwai wata kullalliya da ke gudana a asirce.

 

Wannan  dai ya zo ne bayan da a kwanaki aka rika yada wani faifan bidiyo da a cikinsa aka zargi Gwamna Wike da rushe wani masallaci a garin Fatakwal da kuma ayyana jihar Ribas a matsayin jihar Kiristoci.

Sai dai kuma bayan da wannan takaddama ta dau zafi, Gwamnan ya  musanta wadannan zarge-zarge a kafafen yada labari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply