Home Labarai Gwamnan Zamfara ya yi barazanar ɗauri ga ƴan adawa

Gwamnan Zamfara ya yi barazanar ɗauri ga ƴan adawa

146
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya yi barazanar ɗaure duk ƴan adawar da ke ƙoƙarin ɓata masa suna.

Matawalle wanda ya yi wannan gargaɗi lokacin da ya tarbi wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Zamfara da suka koma PDP, ya ce wasu ƴan adawa na amfani da kalaman tsana da na ɓata suna saboda sun rasa darajarsu ta siyasa.

Ya ce a shirye yake ya ɗaure duk ɗan adawar da ya kasa kare kalaman ɓata sunan da ya yi a kansa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply