Home Sabon Labari Gwamnati ta ce ba a kai wa jirgin kasa na Kaduna hari...

Gwamnati ta ce ba a kai wa jirgin kasa na Kaduna hari ba

93
0

Taskar Guibi: Takaitattun Labarai na 03.01.2020

 

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, bakwai ga watan Jimada Auwal/Ula, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da uku ga watan Janairu, shekarar 2020.

1. Hukumomin reliwe da ‘yan sanda sun ce babu gaskiya a jita-jitar da aka yada jiya cewa wasu ‘yan bindiga sun kai wa jirgin kasa da ke tashi daga Kaduna zuwa Abuja farmaki. Sun ce a lokacin da jirgin ke kan tafiya wani daga waje ya jefi jirgin da dutse ya samu daya daga cikin gilasan tagogin jirgin har ya fashe.

2. Sojojin sama na Nijeriya sun ci gaba da kai farmaki mabuya daban-daban ta ‘yan kungiyar Boko Haram da ke dajin Sambisa, suka kashe da dama daga cikinsu, da lalata wurarensu.

3. Kidinafas sun sace wani basarake a jihar Taraba.

4. ‘Yan sanda sun ceto wasu mutum shida daga hannun kidinafas a jihar Katsina.

5. An kama ainihin wanda ya kitsa fashin da aka so yi wa wani banki a Abuja Allah bai ba su sa’a ba.

6. Wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai farmaki Minchika da ke jihar Adamawa.

7.Kotu ta amincewa EFCC ta ci gaba da tsare Mohammed Adoke na karin kwana goma sha hudu kafin EFCC ta gama kimtsa gurfanar da shi a gaban kuliya.

8. Femi Falana ya rubuta wa Malami yana godon gwamnatin tarayya ta saki Shek Zakzaky.

9. A watan Oktobai kadai kamfanin mai na kasa NNPC ya samu rarar naira biliyan goma sha uku da ‘yan kai daga hada-hadarsa ta kasuwanci.

10. Gwamnatin jihar Kwara ta rushe wani gida na iyalan Saraki da ke Ilori da ake kira ‘Ile Arugbo’ wato gidan jama’a.

11. Kungiyar matasan Arewa ta ce in har adalci ake so a yi a zaman tarayya na kasar nan, to tabbas dan kudu ya kamata a zaba a zaben 2023 ya shugabanci kasar nan. Tunda dan Arewa ya gama mulkinsa na shekara takwas a lokacin.

12. Ana zuba sanyi a cikin garin Kaduna. Ga sanyin can ina ji yana hura usur. Ko kira yake yi a fita a yi guje-guje don wasa jini oho?

 

Af! A nemi jaridar Leadership Hausa ta A Yau Juma’a da za ta fito yau da safe don karanta rubuce-rubucen da na yi a soshiyal midiya daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis. Godiya ta musamman ga editanta Abdulrazak Yahuza Jere, haka nan Zahradeen Umar Dutsen Kura da ke buga rubuce-rubucen nawa a jaridarsa ta DCL, sai Ibrahim Ammani da rubutun nawa ke zama sharhin jaridarsa ta Arewa Dailypost, da sauran dinbin masu yada rubutun nawa kusan kullum zuwa dandali daban-daban, da sauran masoya da MAKIYA duk ina godiya.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply