Home Sabon Labari An saka dokar hana fita a Kaduna

An saka dokar hana fita a Kaduna

275
0

Sanarwar da Kwamishinan Tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya fitar a yammacin Asabar din nan ta ce dokar ta fara aiki nan take. Sai dai ba duka garin Kaduna abin ya shafa ba. Sanarwar ta ce unguwannin da dokar hana.

Sanarwar ta ce unguwannin da dokar hana fitar ta shafa sun hada da Barnawa, Kakuri da Television Maraban Rido, Sabon Tasha, Narayi da Ungwan Romi.

Gwamnatin Kaduna ba ta bayyana dalilin sanya dokar ba. Sai dai ta umurci jami’an tsaro su kama, su kuma hukunta duk mutumin da suka samu a waje da sunan karya dokar.

Sai dai wani mazaunin unguwar Barnawa ya shaida wa DCL Hausa cewa wasu mutane ne suka barke wani katafaren rumbun tara abinci na gwamnati da aka fi sani da Gidan Gona suka kwashi kayan abincin tallafin corona da gwamnati ba ta kai ga rabawa ba, abin da ya haifar da sare-sare a tsakanin matasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply