Gwamnatin Nijeriya ta ce ta fara shirin daina amfani da rahoton auna kwazon ma’aikatan gwamnati da ake fitarwa na shekara-shekara .
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Misis Folasade Yemi-Esan, ce ta bayyana haka a Abuja.
Folashade ta ce a madadin haka, gwamnati za ta bijiro da wani sabon tsari da zai maye gurbinsa wanda zai zamo mizani da za a rika gane kwazon ma’aikatan.
