Home Noma da Kiwo Gwamnati za ta sayi duk alkamar da aka noma daga manoma

Gwamnati za ta sayi duk alkamar da aka noma daga manoma

146
0

Gwamnatin jihar Sokoto ta kulla yarjejeniyar hadin guiwa tsakaninta da babban bankin Nijeriya CBN don lalubo hanyoyin da za a inganta noman alkama a jihar.

Jami’an babban bankin sun ziyarci jihar Sokoto domin ganin irin albarkatun kasa da Allah ya baiwa jihar da kuma gabatar da wannan shirin noman alkama na kasa baki daya domin bunkasa noma da kasuwancinta.

Shirin dai Gwamnatin tarayya ce ta kirkiro da shi domin cike gibin da ke akwai akan wannan sashe.

A cewar jami’in babban bankin Mr. Chika, wannan karo duk manomin da ya noma alkamar za su saye tun daga gonarsu, haka ma sun shirya biyan duk wata matsala da aka fuskanta lokacin gudanar da noman domin kada manomi ya yi asara.

Kwamishinan gona a jihar Sakkwato Arzika Tureta yace gwamnati za ta taimaka wa manoma don ganin sun cimma nasara.

Tuni dai manoma ke cike da fatan Allah ya tabbatar da wannan kuduri.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply